Luke 14

Yesu a Gidan Bafarisiye

1Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau. 2A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu. 3Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa, ya ce, “Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?” 4Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, saʼan nan ya sallame shi.

5Sai ya tambaye, su ya ce, “In wani a cikinku yana da ɗa, ko bijimi da ya faɗa a rijiya a ranar Asabbaci, ba za ku cire shi nan da nan ba?” 6Suka rasa abin faɗi. 7Da ya lura da yadda baƙi suna zaɓan wuraren zama masu ban girma a tebur, sai ya faɗa musu wannan misali, ya ce; 8“In wani ya gayyace ka bikin aure, kada ka zaɓi wurin zama mai ban girma, don wataƙila akwai wani da ya fi ka girma, da aka gayyata. 9In kuwa haka ne, wanda ya gayyace duk biyunku, zai zo ya ce maka, ‘Ka ba wa mutumin nan wurin zamanka.’ Ka ga, an ƙasƙantar da kai, kuma dole ka ɗauki wuri mafi ƙasƙanci. 10Amma in an gayyace ka, ɗauki wuri mafi ƙasƙanci, don in wanda ya gayyace ka ya zo, zai ce maka, ‘Ka hawo nan aboki a wuri mafi girma.’ Wannan zai ɗaukaka ka a gaban dukan yaʼuwanka baƙi. 11Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Shi wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”

12Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, “Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ʼyanʼuwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu. 13Amma lokacin da ka kira biki, ka gayyaci matalauta, da guragu, da shanyayyu, da makafi. 14Ta haka, za ka sami albarka. Ko da yake ba za su iya biyan ka ba, za a biya ka a ranar tashin masu adalci daga matattu.”

Misali na Babban Biki

15Da jin haka, sai wani da yake tare da shi a tebur ɗin, ya ce wa Yesu, “Mai albarka ne wanda zai ci abinci a bikin nan a mulkin Allah.”

16Yesu ya amsa, ya ce, “Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa. 17Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa ya je ya ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, don an shirya kome.’

18“ Amma sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farkon ya ce, ‘Na sayi gona yanzun nan, dole in je in ga yadda take, ina roƙonka ka yi mini haƙuri.’

19“ Wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma yanzun nan, ina kan hanyata ke nan in gwada su, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’ 20Har yanzu wani ya ce, ‘Na yi aure yanzun nan, don haka ni ba zan iya zuwa ba.’

21“ Bawansa ya dawo ya gaya wa maigidansa wannan. Sai maigidan ya yi fushi, ya ba da umarni ga bawansa, ya ce, ‘Ka fita da sauri, ka bi titi-titi da lungu-lungu na garin, ka kawo matalauta, da guragu, da makafi, da shanyayyu.’

22“Bawan ya dawo, ya ce, ‘Ranka yǎ daɗe, an yi abin da ka umarta, amma har yanzu da sauran wuri.’

23“Maigidan ya ce wa bawansa, ‘Ka je kan hanyoyin da layi-layi na karkara, ka sa su shigo, don gidana ya cika.’ 24Ina gaya muku, babu ko ɗaya daga cikin mutanen nan da aka gayyata da zai ɗanɗana bikina.”

Wahalar Rayuwar Almajiri

25Taron mutane mai yawa suna tafiya tare da Yesu, sai ya juya ya ce musu, 26“Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ʼyaʼyansa, da ʼyanʼuwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. 27Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.

28“In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don ya ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin. 29Gama in ya sa tushen gini, amma bai iya gamawa ba, duk wanda ya gani zai yi masa baʼa, 30yana cewa, ‘Wannan mutum ya fara gini, amma bai iya gamawa ba.’

31“Ko kuma, wane sarki ne, in zai je yaƙi da wani sarki, ai, yakan fara zama ne, ya duba ya ga, ko da mutane dubu goma, shi zai iya karawa da mai zuwa da dubu ashirin? 32In ba zai iya ba, to, tun suna nesa, zai aika da wakilai, su je neman sharuɗan salama. 33Haka nan fa, kowane ne a cikin ku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba.

34“Gishiri fa yana da kyau, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? 35Ba shi da wani amfani, ko ga ƙasa, ko ga juji, sai dai a zubar da shi. ‘Duk mai kunnen ji, yǎ ji.’ ”

Copyright information for HauSRK